Gwamnatin Najeriya ta amince cewa kudin tallafin man fetur zai kai Naira Tiriliyan 5.4 a shekarar 2024, duk da ikirarin da aka yi a baya na cewa Ta cire Tallafin gaba daya.
Alfijir labarai ta ruwaito ministan Kudi Wale Edun ya bayyana wannan adadi yayin gabatar da rahoton Accelerated Stabilization and Advancement Plan (ASAP). Rahoton ASAP na da nufin magance manyan kalubalen da suka shafi ayyukan yin garambawul da kuma karfafa ci gaba a sassa daban-daban na tattalin arziki.
Edun ya bayyana cewa, “A halin yanzu, ana hasashen kashe kudaden tallafin man fetur zai kai Naira Tiriliyan 5.4 a karshen shekarar 2024. Wannan karin girma ne daga Naira tiriliyan 3.6 a shekarar 2023 da kuma Naira tiriliyan 2.0 a shekarar 2022.”
Sabanin haka, Heineken Lokpobiri, karamin minista a ma’aikatar albarkatun man fetur, ya tabbatar a lokacin wani taron manema labarai na baya-bayan nan da ministocin suka yi cewa an cire tallafin man gaba daya. “Zan iya tabbatar da cewa tallafin ya tafi; a hukumance, babu tallafi. Ina so in bayyana cewa babu wani tallafi a kasar a yau,” inji shi.
Sai dai Festus Osifo, shugaban kungiyar ‘yan kasuwa, ya bayyana a watan Afrilu cewa gwamnati na ci gaba da Biyan tallafin man fetur.
Cire tallafin man fetur da shugaba Tinubu ya sanar a watan Yunin 2023 ya haifar da tashin gwauron zabin farashin man fetur daga Naira 250 kan kowace lita zuwa sama da N500. Tun daga lokacin, farashin ya ci gaba da hauhawa, inda ya kai matsakaicin Naira 702 a kowace lita a watan Afrilun 2024.
Tasirin cire tallafin man fetur da tsarin tafiyar da Naira da aka aiwatar a watan Yunin 2023 sun ba da gudummawar hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya zuwa kashi 33.69% da hauhawar farashin abinci zuwa kashi 40.53% kamar na Afrilu 2024.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj