Gwamnan jihar kano, Abba K Yusuf ya hadu da iyayen wayannan yaran a wannan dare a ofishin sa dake fadar Gwamnatin jihar Kano, kamar yadda ya bayar da umarnin a nemo su.
Wayannan yara sune wadanda gwamnan ya gani jiya jiya Asabar akwance akan titi Lodge Road da karfe 2 na dare yayin da ya fita duba aiki a wannan dare.
Gwamnan ya ba da Umarnin a bawa iyayen wayannan yara wadatattun kayan abinci tare da basu kudi domin yin cefane dan ciyar da wayannan yara, inda kuma Gwamnan yai Alkawarin bawa iyayen yaran kudi domin jari suyu Sanaβa, kuma dai Gwamnan ya bayar da umarnin Gaggawa domin a sa yaran a makaranta mai kyau tare da dukkan kannansu da suke gida basa zuwa makaranata.






Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan π
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group ππ
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD