‘Yan sanda sun kama mutum 22 da ake zargi da kashe matafiya a Mangu jihar Filato

FB IMG 1717108061650

‘Yan sandan Nijeriya a ranar Lahadi sun kama wasu mutum 22 da ake zargi da kai harin da ya yi sanadin mutuwar aƙalla mutum goma sha biyu a Jihar Filato da ke takiyar Nijeriya.

Sanarwar da ‘yan sanda suka fitar ta ce wasu fusatattun matasa ne suka afka wa bas ɗin a yankin Mangu da ke Jihar Filato.

Fasinjojin sun taso ne daga Zaria inda suke hanyarsu ta zuwa wurin biki sai suka yi ɓatan hanya a ranar Juma’a da dare, lamarin da ya yi sanadin aka afka musu.

‘Yan sandan sun bayyana cewa an ceto mutum 21 daga hannun “fusatattun matasan,” sannan kuma an kashe wasu fasinjojin, ba tare da yin ƙarin bayani kan lamarin ba.

Ƙungiyoyin kare haƙƙin bil’adama irin su Amnesty International tuni suka sanar da mutuwar mutum 12 inda suka ce an kashe su ne nan take.

Tun bayan aikata wannan ɗanyen aikin, tuni mutane suka yi ta nuna ɓacin ransu game da faruwar wannan lamarin a shafukan sada zumunta tare da kira ga hukumomi su ɗauki mataki mai tsauri kan masu hannu a ciki.

Gwamnan Jihar Filato Caleb Mutfwang a sanarwar da ya fitar a ranar Asabar, ya buƙaci jami’an tsaro su ɗauki mataki tare da tabbatar da cewa an yi adalci don guje wa afkuwar irin haka a nan gaba.

Yankin arewa maso tsakiyar Nijeriya na ƙara faɗawa a cikin rikici a ‘yan kwanakin nan.

Ko a cikin watan nan na Yuni sai da aka kashe aƙalla mutum 100 a Jihar Benue mai maƙwabtaka da Filato.

Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *