Yadda wasu ‘Yan Sanda Suka Yi Garkuwa Da Wani Mazaunin Abuja Suka Yashe Fiye Da Naira Miliyan 20 A Asusunsa

FB IMG 1703222676383

A yayin da sace-sacen jama’a ke kara kamari a babban birnin tarayya Abuja, an kama wasu jami’an ‘yansanda bisa zargin kwatar naira miliyan 29.9 daga hannun wani mazaunin Abuja.

Alfijir labarai ta rawaito lamarin, a cewar Harrison Gwamnishu, dan takarar jam’iyyar Labour Party (LP) a zaben 2023, ya faru ne a watan Janairu.

Gwamnishu, kamar yadda ya bayyana a wani faifan bidiyo ta shafinsa na X (Twitter) cewa, jami’an ‘yansandan sun yi garkuwa da dan kasuwar ne a Abuja inda suka tsare shi har sai da ya mika musu dukkan kudaden da ke cikin asusun bankinsa.

Daga nan ne suka dage sai ya kira ‘yan’uwa da abokan arziki su ci gaba da tura masa kudi kafin a sako shi.

Da yake tsokaci kan wannan lamari a ranar Talata, kakakin rundunar, Olumuyiwa Adejobi, yayin da yake tabbatar da kama wasu daga cikin masu laifin, ya bayyana cewa rundunar na ci gaba da bincike kan lamarin kuma za ta tabbatar da adalci.

“Muna kan binciken lamarin, kuma za a yi adalci, kamar yadda aka kama wasu da ake zargi.” kamar yadda ya rubuta.

Daily Trust

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *