
Alfijr ta rawaito Jami’an tsaro sun yi wa hedkwatar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da ke Jihar Kano Hajj camp kawanya da da motocin silke da karafa.

Wakilin Aminiya ya gane wa idanunsa yadda jami’an suka rufe ilahirin hanyoyin da ke kaiwa ga hedkwatar.
Sai dai kodayake an kyale shi ya wuce shingen, amma daga bisani an hana shi shiga babbar kofar shiga ciki, inda suka shaida masa sai karfe 1:30 za a bude wajen.

Kazalika, hatta mazauna yankin sun shiga tsilla-tsilla saboda an hana su shiga gidajensu.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ