Ya Kamata A Zabtare Albashinmu A Bawa Malaman Jami’a, In Ji Sanata Ali Ndume

Alfijr ta rawaito Sanata Ali Ndume ya shawarci gwamnatin tarayya da ta zabtare albashin ‘yan majalisa da kashi 50 cikin 100 domin biyan malaman jami’o’i da ke yajin aiki kuɗaɗensu.

Sanata Ndume da ke wakiltar Borno ta kudu a majalisar dattijai ya shaida hakan ne a birnin Maiduguri lokacin wani taro.

Sanatan ya bayyana cewa wannan abu ne da ya shafi kasa baki ɗaya, kuma dole a wasu lokutan a ɗau matakan ceto ‘yan kasa da ilimi.

Wannan Kiran da sanatan ya yi ya faru ne adaida lokacin da malaman jami’i’oi ke korafin cewa rabin albashinsu aka basu bayan sun janye yajin aiki.

Dan majalisar dai na cewa lokaci ya yi da ya kamata a shawo kan matsalolin da ke durkusar da fanin ilimi a Najeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *