Babbar Kotun Tarayyar Nigeria Ta Yi Watsi Da Hukuncin Da Aka Yi Wa Shugaban EFCC

Alfijr ta rawaito babbar kotun tarayya da ke zamanta a babban birnin tarayya Abuja ta yi watsi da hukuncin da aka yiwa shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa da laifin raina Kotu.

Alkalin kotun Mai shari’a Chizoba Oji ce ta ya yi watsi da hukuncin a ranar Alhamis, bayan sauraron ƙorafin da shugaban hukumar yaƙi da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati ya shigar.

Binciken Kotun ya gano cewar ba za a iya cewa Bawa ya raina kotu a lokacin da aka yanke hukuncin ba, kasancewar ya riga ya bayar da umurnin a mayar wa wanda ya shigar da ƙarar motarsa ƙirar Range Rover.

Hakazalika Kotun ta ce takardu sun nuna cewa an fara shirin mayar wa mai ƙorafin motarsa da kuma kuɗi naira miliyan 40.

A ranar Talata ne mai shari’a Chizoba Oji ta yanke hukuncin cewar EFCC ta raina kotu ta hanyar ƙin bin umurnin hukuncin da ya ce a mayar wa wani mutum motarsa da kuma kuɗi naira miliyan 40.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/KrigvNKcneVBHxctLUQ0ux

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *