Alfijr ta rawaito daruruwan mutane ne suka taru a kan titunan Landan, babban birnin kasar Ingila, domin nuna adawa da manufofin gwamnati kan Tsarin Kiwon Lafiya na Kasa (NHS).
Masu ra’ayin sauyi sun yi tattaki zuwa titin Downing, inda ofishin Firaminista “Lamba 10” yake, domin goyon bayan ma’aikatan NHS da ke yajin aiki.
Masu zanga-zangar sun bukaci da a kara albashin ma’aikatan kiwon lafiya tare da yin kira ga gwamnati da ta biya masu jinyar marasa lafiya a asibiti albashi mai kyau.
Daruruwan masu jinyar marasa lafiya a Ingila sun yanke shawarar shiga yajin aikin na sa’o’i 48 a jiya.
Ma’aikatan jinya, mambobin Kungiyar RCN sun bar asibitoci 55 bayan da gwamnati ta ki yin karin albashin da suka nema.
TRT Hausa
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Laba