An Sanya Ranar Da Za’a Fara Jigilar Maniyyatan Hajjin Bana 2023 – GACA

Alfijr ta rawaito hukumar Jiragen Sama ta ƙasar Saudiyya (GACA), ta saki jadawalin yadda aikin jigilar maniyyata da alhazai zai kasance yayin Hajjin 2023.

Jadawalin an fitar da shi ne, yau Alhamis, inda ya nuna cewa za a bude filin jirgin sama ga jirgi na farko aranar Lahadi, 21 ga Mayu, 2023.

GACA ta ƙara da cewa za a rufe filayen jirgin saman bayan dawowar jirgin karshe wajen kammala jigilar alhazan zuwa gida a ranar Alhamis, 22 ga Yunin 2023.

Yayin da jigilar alhazai da ga Saudiyya zuwa gida zai fara a ran Lahadi, 2 ga Yulin 2023, sannan a kammala ran Laraba, 2 ga Agusta.

Kazalika, GACA ta shawarci kasashen da za su yi Hajji da su miƙa bayanan da ake buƙata daga gare su kada ya wuce ranar Litinin, 29 ga Rajab wanda ya yi daidai da 20 ga Fabrairu, 2023.

Maniyyata sama da miliyan biyu ake sa ran za su yi Hajji bana a Masarautar Saudiyya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *