Wata Sabuwa: INEC Ta Bankado Wasu Katunan Shaida Na Jabu Ga Jami’an Tsaro

Alfijr ta rawaito Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta koka kan katin shaidar jabu ga jami’an tsaro da ke aikin zabe.

Okoye ya ce an ja hankalin INEC kan katin shaida na jami’an tsaro mai dauke da suna da tambarin hukumar mai dauke da rubuta “Complete Access” da ja a kasan sa.

“Muna so mu bayyana cewa katin shaida bai fito daga Hukumar ba.

Katin shaida na jami’an tsaro da ke aikin zabe jami’an tsaro ne suka bayar ba Hukumar ba.

“Duk wanda ke dauke da katin shaida da ake zargin hukumar ta bayar na jami’an tsaro zai iya yin aiki ba bisa ka’ida ba.

Irin wannan mutumin yana da alhakin a kama shi kuma a tuhume shi.

Ana sanar da jama’a game da wannan mataki na wasu bata gari da kuma kai rahoto ga jami’an tsaro,” in ji Okoye.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *