Wata Jami’ar Nijeriya Ta Hana Ɗalibai Amfani Da Wayoyin Zamani

Alfijr ta rawaito Jami’ar Bingham da ke Karu, a Jihar Nasarawa ta fitar da sanarwar hana dalibai amfani da wayoyin zamani.

Sanarwar, mai ɗauke da kwanan wata, 18 ga Janairu ta sanar da ɗalibai cewa an ɗauki matakin ne biyo bayan karya dokokin makaranta game da amfani da wayar hannu da daliban suke ne.

“Bayan karya dokoki akai-akai wajen amfani da wayoyin hannu, wanda ya saɓa wa sashe na 5.14 karamin sashe na I, II da III na littafin jagoranci ga dalibai, an haramta amfani da wayoyin cikin gaggawa. In Ji sanarwar.

“Za a kwace wayoyin waɗanda su ka karya wannan doka kuma za su fuskanci hukunci da ya dace.”

Sanarwar ta ƙara da cewa bayan hana amfani da wayar hannu ta zamani, jami’ar ta ce dalibai na iya amfani da kwamfutocin su.

“Eh, mun hana amfani da wayoyin zamani kamar yadda aka bayyana a cikin bayanin magatakarda amma muna ba da izinin amfani da kwamfyutoci,” in ji sanarwar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *