Alfijr ta rawaito wasu ƴan Sandan kwalli da ake zargin sun harbi wani matashi mai suna Muntari a wuyansa biyo bayan tsama dake tsakaninsu.
Ƴan Sandan da ake zargin da yin wannan aika-aikar sun hada da wani mai suna Holanda da Gaddafi wanda suke aiki da ofishin kwalli dibishin.
A tattaunawar Jaridar Alfijr Labarai da ɗaya daga cikin yan uwan Marigayin mai suna Yakubu ya yi mana bayanin faruwar lamarin dalla-dalla.
Ya fara da cewar, shekeranjiya Ɗan Sanda Holanda yayi ikirarin sai sun kashe Muntari biyo bayan wani sa insa da ya hada su da babu wanda ya san menene, jiya juma’a bayan ya dawo daga Rimin Gado siyo dusa wajen goma na dare suka zo suka harbe shi a wuyansa ba fada ba kokawa ba hayaniya a lokacin.
Mun kokarin yan sandan su bamu dama akan dan uwanmu amma sunki kememe, don haka muke rokon Mahukunta da su bi mana hakkin dan uwanmu.
A zantawar Jaridar Alfijr Labarai da kakakin hulɗa da jama’a na rundunar ƴan Sandan jahar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce mana yana kan bincike akan lamarin da zarar ya kammala zai sanar da mu.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇