Bayan Wani Hadari Da Yayi Sanadin Mutuwar Mutun 6 Matawalle Ya Dakatar Da Yakin Neman Zabensa

Daga Shu’aibu I. Wanzan

Alfijr ta rawaito gwamna Bello Mohammed (Matawallen Maradun) ya dakatar da gangamin yakin neman zaben sa a karamar hukumar Bukkuyum domin alhinin rasuwar mutane shidda da suka yi mummunan hatsarin mota Kan hanyar Gummi zuwa Bukkuyum a daren juma’a.

Hakan yana kun shene cikin wata takar da mai dauke da sa hannun,
Zailani Bappa Mashawarci na Musamman ga mai daraja gwamna Kan Harkokin yada labarai da sadarwa.

Ya kara da cewa hatsarin ya afku ne bayan sallar Magariba a lokacin da wasu motoci uku suka yi taho mugama da juna, inda rahotanni suka ce mutane shida ne suka rasa rayukansu.

Zailani ya kara da cewa, Biyar daga cikin gawarwakin an yi musu sallah, bayan sallar Juma’a a garin Bukkuyum inda mai daraja gwamna da tawagarsa suka halarta.

Tun da farko Gwamna Matawalle yana nufin kaddamar da gangamin yakin neman zabensa a garin Bukkuyum bayan Sallar Juma’a, amma ya yanke shawarar dakatar da taron don girmama rayukan da suka rasu a Jihar..

Ya ce a maimakon haka sai ya ziyarci mai martaba sarkin Bukuyum Alhaji Mohammad Usman a fadarsa, tare da mika ta’aziyya ga iyalai da al’ummar garin Bukkuyum baki daya, ya ce Allah madaukakin sarki haka ya tsara lamarin cikin hikimarsa, kuma hikimar Allah ita ce mafi alherin zabi ga muminai.

Ya ce Kafin gwamna matawalle ya tashi daga fadar Mai martaba ya umurci tsohon mataimakin gwamnan jihar, Malam Ibrahim Wakkala Liman domin yin addu’a ta musamman ga marigayin.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *