Wani Ɗan Sanda Ya Harbe Matarsa Da kwartonta

Alfijr ta rawaito an kama wani jami’in ɗan sanda mai suna Mmutle a Afirka ta Kudu bisa hannu a kisan matarsa da wani ɗan shekara 30 mai suna Katlego da yake zargin kwartonta ne.

Bayanai na cewa ɗan sandan ya ga matarsa tare da kwarton ne a gidan ƙawarta inda kuma ya buɗe musu wuta kamar yadda jaridar IOL ta wallafa.

Mai magana da yawun hukumar bincike ta ƴan sanda mai zaman kanta Lizzy Suping ta ce lamarin ya faru ne da yammacin ranar Talata.

Suping ta ce jami’in ya miƙa kansa ne ga ƴan sanda a ranar Laraba.

Kakakin rundunar ƴan sandan Brigadiya Sabata Mokgwabone ya ce ɗan sandan ya je gidan inda ake zargin ya buɗe wuta lamarin da ya hallaka mutumin mai shekara 30 da kuma matar tasa, wadda ita ma ƴar sanda ce.

Zuwa yanzu dai hukumomi sun ce an ƙaddamar da bincike kan lamarin.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *