
Daga Aminu Bala Madobi
Alfijr ta rawaito cewar dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a jihar Oyo, Teslim Folarin ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi a Ibadan babban birnin jihar.
A cewar shedun gani da ido, mai ba Folarin shawara na musamman kan harkokin labarai, Yekeen Olaniyi ya bayyana hakan a wata tattaunawa ta wayar tarho a ranar Juma’a, 17 ga Maris, 2023.

Ya ce wasu ‘yan bindiga da suka rufe fuska sun kai farmaki gidan kakannin sa da ke unguwar Oja’gbo a karamar hukumar Ibadan ta Arewa-maso-gabas a jihar da misalin karfe 8 na dare domin neman Folarin wanda ya shirya ganawa da ‘yan uwa.
Olaniyi ya ce, “Oga ya tsallake rijiya da baya da wani yunkurin kashe shi da aka yi masa a yammacin yau.

Kamar yadda kuka sani, shine wanda ke wakiltar iyalinsa a layin Olubadan a matsayin Asaju Olubadan. Don haka, ya kamata ya gudanar da taron tsakanin karfe 6:30 zuwa 7 na yamma amma saboda yana wani shiri a gidan rediyo, bai iya samun lokacin ba.
“Bai bar gidan rediyon ba sai da misalin karfe 8:40 na dare. Don haka ‘yan bindigar suka mamaye yankin da misalin karfe 8 na dare suna tunanin yana nan ne suka fara harbe-harbe ba ba kakkautawa inda suka raunata mutane da dama.”

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ