Hukumar zaɓen Najeriya INEC ta musanta rahotanni cewa ta yi watsi da ɗaukaka ƙarar da aka yi game da zaɓen gwamnan Kano na 2023.
Alfijir Labarai ta rawaito cikin wata sanarwa da kwamishinan INEC kan yaɗa labarai da ilmantar da masu zaɓe na ƙasa, Sam Olumekun ya fitar da yammacin ranar Lahadi, hukumar ta ce manufarta kan batu irin na shari’ar zaɓen Kano, ba ta canza ba.
Ta ce a duk wata shari’a da mai ƙara ya haɗa da hukumar zaɓen ta Najeriya, to akwai wajabci a kan INEC ta mayar da martani cikin lamarin kamar yadda ya dace Don haka a cewar sanarwar tuni ta umarci lauyoyinta su ci gaba da bin kadin shari’ar kamar yadda manufofin INEC suka tanada.
Matakin na zuwa bayan wata sanarwar hukumar ta bayyana a shafukan sada zumunta, tana iƙirarin cewa INEC ta tsame hannu daga shari’ar zaɓen gwamnan Kano da aka ɗaukaka ƙara.
Sanarwar farko wadda jami’in sashen shari’a na INEC a jihar Kano, Suleiman Alkali ya fitar na cewa hedkwatar INEC ta ba da umarnin janyewa daga shari’ar, saboda babu wani dalili na ɗaukaka ƙara.
Sai dai sanarwar INEC ta biyu daga hedkwatarta da ke Abuja wadda kuma hukumar ta wallafa a shafukan sada zumunta, ta ce hankalinta ya kai ga wata sanarwa da jami’inta na sashen shari’a a ofishinta da ke Kano ya fitar wanda ke nuni da cewa hukumar ta janye ƙarar zaɓen gwamnan Kano da ta yi.
“Muna so mu bayyana cewa jami’in ba shi da hurumin yin hakan. Kuma tuni muka janye sanarwar, sannan kuma an tsawatar wa jami’in,” in ji sanarwar. INEC ta ce jama’a su yi watsi da sanarwar da ke cewa ta janye daga shari’ar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo