Takaitattun labaran Yammacin Asabar 07/10/2023, 22/03/1445AH

best seller i

Daga Baba Usman Gama

Gwamnatin Tarayya ta sanar da dakatar da shirin N-Power har sai abin da hali ya yi..

Kotun Daukaka Kara ta dawo wa dan Majalisar Tarayya na NNPP daga mazabar Tarauni a Jihar Kano, Mukhtar Umar Yarima, kujerarsa da kotun sauraron kararrakin zabe ta kwace.

Jam’iyyar NNPP a Kano ta ce babban kuskuren da Tinubu ya yi shi ne zaban Ganduje shugaban APC.

Gwamnatin Zamfara za ta kafa kwamitin ƴan sa-kai don samar da tsaro.

Yan bindiga sun kai hari a Unguwar Dandali da ke Zariya a jihar Kaduna inda suka kashe mutum 4 tare da raunata wasu mutum 5.

Lauyan NNPP ya ce nasarar da Kotu ta ba Nasiru Yusuf Gawuna ta ci karo da doka da tsarin mulki.

Kwastam ta kama kwantenoni 20 ɗauke da tumatir ɗin da ya lalace a ruwan Legas.

Isra’ila ta kashe Falasdinawa 198 bayan harin Hamas ya kashe ‘yan kasar 70.

Ayatollah Khamenei na Iran ya goyi bayan harin da Hamas ta kai wa Isra’ila sannan ya sha alwashin cigaba da mara wa kungiyar baya har sai Falasdinawa da Birnin Kudus sun samu ‘yanci.

An kashe fursunoni shida a gidan yari a Ecuador.

Musulmai da Kirista sun yi gangamin adawa da halasta auren jinsi a Kenya.

Kotun Congo ta yankewa dan majalisa hukuncin kisa kan laifin cin amanar kasa.

EPL: Manchester United ta sami nasara akan Brendford da ci 2:1 a wasan yau.

EPL: Chelsea ta sami nasara akan Burnley da ci 4:1 a wasan jiya.

Laliga: Real Madrid ta sami nasara akan da ci 4:0 a wasan yau.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo

One Reply to “Takaitattun labaran Yammacin Asabar 07/10/2023, 22/03/1445AH”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *