Daga Baba Usman Gama
Gwamnatin jihar Katsina za ta tura ɗaliban makarantun gwamnati karatu waje.
Wani mutu tabin hankali ya kashe mutum 8 sannan ya jikkata wasu da dama a Karamar Hukumar Shelleng a Jihar Adamawa.
Shugaban kungiyar yace PENGASSAN Farashin man fetur ba zai daidaita ba sai dala ta sauko.
‘Yan sanda sun fatattaki wasu yan fashi da suka kai hari Otal ranar Jumu’a a ƙaramar hukumar Sagamu ta jihar Ogun.
Gwamnan Kano ya dauki hayar fitaccen lauyan nan, Cif Wole Olanipekun (SAN) domin ya wakilci shari’arsa a Kotun Daukaka Kara.
Sojoji sun kama ‘yan ta’adda 91 a Filato da kudancin jihar Kaduna a cikin kwanaki 10.
Kwastam ta kama durom 1,600 na gurbataccen tumatir da aka shigar da shi Nijeriya daga Spain.
An kama mutum 29 da makamai da kayan maye lokacin Takutaha a Jihar Kano.
Najeriya za ta ciyo bashi don farfado da darajar Naira.
Motocin agajin abinci sun makale kan iyakar Nijar.
Kudin-cizo ya tilasta wa Faransa rufe makarantu 7 sakamakon fargabar bazuwarsa a yankuna daban-daban.
Jami’ar Birtaniya za ta fara digiri na biyu a fannin tsafi.
An yi zanga-zangar ƙin jinin ƴan luwaɗi a Kenya.
Barcelona na duba yiwuwar ɗauko aron Messi, a watan Janairu idan ƙungiyarsa Inter Miami ta kasa samun gurbin wasannin Kofin Amurka na MLS.
Uwargidan tsohon kocin Manchester United Alex Ferguson ta mutu.
Samuel Eto’o na fuskantar zarge-zarge a Kamaru
Laliga: Athletic Club ta sami nasara akan Almeria da ci 3:0 a wasan jiya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/K8z1chFesJeCf99QehWJPo