Tsohon Minista Fantami ya sanar da tara Miliyan 50 don biyan yan ta’adda kudin fansa

FB IMG 1705304855131

Bayan kashe Nabeeha, barayin sun kara kudin fansa zuwa Naira miliyan 100, inda suka yi barazanar kashe sauran ‘yan’uwan idan har ba a biya su kudin ba.

Alfijir labarai ta rawaito ‘yan bindigar da suka kai hari a Ƙaramar Hukumar Bwari a birnin tarayya Abuja a daren Ranar Talata, Inda suka yi awon Gaba da wani mutum da ‘ya’yansa mata Guda shida.

Sun saki mahaifin kuma sun nemi ya biya Naira miliyan 60 domin karɓo ‘ya’yansa mata.

Masu laifin sun ba da wa’adin ranar Juma’a domin a biya su kudin fansar.

Amma ‘yan uwa sun tara Naira miliyan 30, inda suka ki Amincewa suka kashe Nabeeha.

Bayan kashe Nabeeha, barayin sun kara kudin fansa zuwa Naira miliyan 100, inda suka yi barazanar kashe sauran ‘yan’uwan idan har ba a biya su kudin ba.

‘Yan Najeriya sun samu labarin rasuwar Nabeehah, ‘yar aji 500 a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zari.

A yayin da wannan labari mai cike da bakin ciki ke yawo, tsohon ministan ya bayyana cewa yayi magana da “aboki kuma yan uwa” dake son biyan sauran kuɗin fansa na Naira Miliyan 50 Daga kudin fansa da barayin suka nema.

Ya rubuta: “Alhamdu lil Laah! Ni da kaina ba na goyon bayan biyan kudin fansa ga masu laifi. Sai dai kuma tunda ta tabbata jiya mun rasa ‘yar mu Nabeeha, kuma an yi wa ‘ya’yan mata guda 5 barazana kamar yadda na yi magana da mahaifinta.

“Bugu da ƙari, na yi magana da wani abokina kuma ɗan’uwa wanda ya yi tayin Biyan sauran Naira miliyan 50 nan take.

Na isar da lambar asusun mahaifin ƴan matan ga abokina da yan’uwa su aiko da kuɗin kai tsaye.

Duk wani karin kudin da aka samu uban zai iya amfani da shi wajen yi wa ‘ya’ya mata da sauran ‘yan uwa magani in sha Allahu.” Ya kuma yi addu’a ga masu hannu da shuni tare da addu’ar zaman lafiya a ƙasar.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *