Yadda TB Joshua ya yaudari mutane ta hanyar shirya abubuwan al’ajabi na ƙarya

FB IMG 1705306449463

A karon farko BBC ta bankado yadda marigayi TB Joshau ya rika gudanar da abubuwan al’ajabi na karya da suka ja hankalin miliyoyin mutane zuwa cocinsa.

Faston wanda ake zargi da cin zarafi da azabtarwa tsawon shekaru 20 ya kafa cocinsa na Synagogue Church of All Nations (Scoan) a Lagos fiye da shekaru 30 da suka gabata.

Tauraruwarsa ta haskaka ne a lokacin da ya nuna shi mutum ne mai baiwa wanda kuma zai iya warkar da marasa lafiya.

An nuna yadda ya rika warkar da nakasassu suna tafiya, da wani lokaci da ya yi ikirarin tayar da matacce a wani hoton bidiyo da aka nada. Tare da bayanai daga wadanda ya yi ikirarin cewa ya warkar, duk abubuwa ne da aka nada ta hoton bidiyon VHS da aka tura wa majami’u a fadin duniya.

A shekarar 2004, hukumar da ke kula kafofin yada labarai ta Najeriya ta haramta wa tashoshin yada labarai ta kasar nuna abubuwan al’ajabi na fastoci kai tsaye a gidajen talibijin, abinda ya sa Joshau ya kaddamar da gidan talibijin na Emmaanuel TV a tauraron dan’adam daga bisani kuma ta intanet.

Kafar talibijin dinsa da daularsa ta kafar sada zumunta sun kasance daya daga cikin cibiyoyin sadarwa na kirista mafi bunkasa a duniya.

An rika watsa abubuwm al’ajabinsa ga miliyoyin mutane a duk fadin turai da kasashen nahiyar Amurka da Kudu-maso gabashin Asiya da Afirka.

Miliyoyin mutane ke kallo a shafinsa na YouTube.

Sai dai Joshua wanda ya mutu a 2021 yana da shekara 57, ya kasance mai zamba.

Binciken da BBC ta gudanar wanda ya hada da almajiransa da suka rika yi masa hidima fiye da 25 da suka fito daga Birtaniya da Najeriya da Ghana da Amurka da Afrika ta Kudu da Jamus sun zayyana hanyoyi shida da ya rika yaudarar masu ibada

Sashen gaggawa
Wani sashe na musamman na cocin , da ake kira “sashen gaggawa’’.

Shi ne ke da alhakin shirya abubuwan mu’ujiza su zaman tamkar na gaske. A wannan wurin ne ake tantance marasa lafiya da suka zo neman waraka, kuma a nan ne tawagar za ta yanke shawara a kan wanda za a dauki hoton bidiyonsa kuma Joshau ya yi masa addu’a.

Agomoh Paul wanda ya jagoranci sashen na tsawon shekaru 10, wanda ya rika samun umurni daga Joshua, ya shaida wa BBC cewa “likitoci ne suka horar da tawagar’’.

Shi tsohon almajirinsa ne – daya daga cikin mabiyansa da suka zauna tare da faston a cikin cocin na Scoan.

“Suna sallamar dukkanin masu ciwon daji, mutane masu raunuka da za su iya warkewa su ne ake gabatarwa a matsayin masu cutar Sankara ,” in ji shi.

Almajirai kalilan ne, da aka yarda da su aka ba su damar aiki a sashen na gaggawa.

Su ne suke rubutu a kan alluna da kowane mabiyi ya rike, inda suke ba da cikakken bayanin bogi game da cututtukan. Idan lokacin haduwarsu da Joshua ya yi, za su tsaya a layi a gaban kyamarori kuma a “warkar da su’’

“Tsari ne mai sarkakiya. Ba dukan almajiran ne suka san abin da ke faruwa ba, sirri ne,” In ji Paul.

Magunguna
Duk wani bako dan kasar waje da ya zo coci don a warkar da shi sai ya cika wani wata takardar da zai yi bayani a kan rashin lafiyarsa da kuma magungunan da aka rubuta masa. Za a fada musu su daina shan magungunan amma Joshua ya umurci masu harhada magunguna su sayo irin wannan magani.

Ba tare da saninsu ba za su “zuba magungunan a cikin abin shansu ko lemu,” a cewar Mista Paul, wanda ya ce za a bukaci mutane su sha hadin da ke dauke da tabarrakin Joshua.

Wannan yana nufin yayin da bakin ke zaune a Scoan ba za su yi rashin lafiya ba kuma za su yi ittifaki da baiwar warkarwa na limamin cocinsu.

A cikin shekarun 1990 lokacin da cutar Sida (HIV) ta kai matakin annoba a sassan kasashen da ke kudu da hamadar sahara, Joshua ya fada wa baki cewa su daina shan magungunan da ke rage radadin cutar ta HIV idan sun koma gida

“Na san mutanen da suka mutu saboda sun daina shan magani , kuma wannan abu ne da ya jefa ni cikin damuwa a rayuwata,” in ji wani tsohon almajirinsa, wanda ya nemi a sakaya sunansa.

Tash Ford mai shekara 49 a yanzu, wadda ta je Lagos daga birnin Johannesburg na Afrika ta kudu a 2001 da fatan samun maganin ciwon koda an fada mata cewa ta daina shan magani.

A lokacin an riga an yi mata dashen koda biyu.

Ta yi imanin cewa ta warke sai dai bayan ta koma gida bayan watanni hudu da daina shan magani sai ta rika fama da rashin lafiya har ya kai ga kwantar da ita a asibiti.

Sauya ra’ayin mutane
Madam Ford ta ce a lokacin da take zama a cocin na Scoan ba taba yin shakka ba: ” A gaskiya na yi tunanin abubuwan mu’ujiza ne muke gani. Na ga wani ya tashi daga keken guragu’’

Wata tsohuwar almajirar cocin ta shaida wa BBC cewa bayan an tantance su, za a gaya wa zababbun mabiya cocin cewa su “zuzuta matsalolinsu domin samun warakar ubangiji’’.

“A zahiri an sauya tunanin mutanen,” in ji ta.

Cocin ya riga ya tanadi kekunan guragu da aka tilasta wa mabiya amfani da su.

An gargade su cewa ba za su warke ba sai sun zauna a keken guragun idan suna son su hadu da Joshua.

“Mun fada musu cewa: ‘ Idan kuka fito daga wannan wuri, kuka taka da kafafuwanku, baba ba zai yi muku addu’a ba. In ji Mr Paul.

Wata tsohuwar almajirar cocin , Bisola, wadda ta shafe shekaru 14 tana zaune a cocin ta taba yi wa Joshua rakiya zuwa kasar Singapore a 2006 inda ya je domin gudanar da wani taron addu’oi .

Ta ce ta ga mutanen a keken guragu wadanda suka rika kokarin tashi bayan da faston ya fada wa mabiyansa cewa “tabarrakinsa na cikin filin wasan”.

Sai dai ba a tantance mutanen ba kuma ta ga lokacin da suka rika faduwa, “Na yi kuka. Na yi musu kuka,” in ji ta.

Toshiyar Baki
Wasu almajirai sun yi zargin cewa an tuhume su da neman mutanen da ke bukatar kudi inda suke fada musu cewa su yi kamar wadanda ba su da lafiya.

A lokacin da suka gudanar da wani taron addu’o’i a kasashen waje suna zuwa yankunan da ke fama da bakin talauci don neman talakawa.

“Za mu ce ‘Muna bukatar ku aiwatar da wani yanayi kuma za mu biya ku,” a cewar wata tsohuwar almajira.

“Za mu tanadar musu dakuna a otel, mu gyara musu jiki kuma suna yin abin da aka ce su yi, bayan sun gama muna biyan su,” in ji ta.

Gabanin taron adu’o’in za su fada wa Joshua wuraren da suka ajiye mutane da kuma tufafin da suka saka domin ya san wanda zai yi abin mu’ujiza a kansa.

Takardun likita na bogi
“Mu’ujiza warkarwar” da ake yadawa miliyoyin mutane a kai-a kai sun hada da takardar gwaji da ta nuna cewa an warkar da mutane daga cutar AIDS da cututtuka kamar sankara. An yi hira da likitoci ta kyamara da suka tabbatar da haka.

A 2000 wani dan jarida a Najeriya Adejuwon Soyinka ya ruwaito cewa takardun shaidar likita na bogi ne sai dai Joshua ya yi watsi da binciken.

Sai dai ya zuwa yanzu wasu sun yi amannar cewa sun samu waraka.

“Dukkan abin da aka gudanar da shi a mataki ne kuma na bogi ne,” in ji Mista Paul.

“Babu wani abu da ya faru a cikin harabar da Joshua bai sani ba,” in ji shi.

Amfani da hoton bidiyo wajen sauya tunanin mutane
An yi amfani da hoton bidiyo wajen nuna abubuwan “al’ajabi sanan aka gyarasu don su yi kama da cewa waraka ta faru nan take.”

An hada abin da ya faru a baya da yanzu domin nuna ikonsa na ban mamaki amma a zahiri an dauki hoton ne a cikin shekara guda ko watanni

‘’Abin da kuke gani a talibijin shi ne abin da ya faru a baya da kuma yanzu babu takamaimen lokacin da abin ya faru’’ in ji Bisola wadda ita ce babbar editar tace fina-finai ta cocin na tsawon shekaru biyar.

“Abin da mutane ke gani…ba gaskiya ba ne. Zamba ce,’’ in ji ta game da hotunan bidiyon da aka yadda karkashin jagorancinta.

“Ina magana ne a matsayin wadda ta san sirrin cocin,” In jita.

BBC ta tuntubi cocin na Scoan kan zargen- zargen da aka yi mata a binciken . Ba ta ce komai ba amma a baya ta musanta zargin da aka yi wa Joshua.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *