Majalisar dattawa ta yi sammacin manyan hafsoshin tsaron Najeriya game da kalubalen tsaro da ke ci gaba da ta’azzara a fadin kasar.
Alfijir labarai ta rawaito yan majalisar sun yi wannan kira a karkashin murya guda bayan wani zaman gaggawa da suka yi bayan dawowarsu bakin aiki karon farko a wannan shekarar.
Majalisar dattawan ta yi zaman gaggawar ne bayan da shugaban masu rinjaye na majalisar Sanata Opeyemi Bamidele ya gabatar da kuduri a madadin sanatocin kan yanayin tsaro a Najeriya.
Bayan shafe kusan sa’a biyu suna taron sirri, majalisar ta sake haduwa tare da yanke shawarar gayyato manyan hafsoshin tsaro a mako mai zuwa game da karuwar rashin tsaro a kasar.
Manyan hafsoshin tsaron sun hada da babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa da shugaban rundunar sojin kasa, Leftenant Taoreed Lagbaja da shugaban rundunar sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar da shugaban rundunar sojin ruwa Vice Admiral Emmanuel Ogalla.
Majalisar ta kuma dage zamanta zuwa 6 ga watan gobe na Fabarairu domin bai wa yan majalisar damar yin zabe a zaben cike gurbi na ranar Asabar.
A baya-bayan nan, an ga karuwar matsalar tsaro a Abuja, babban birnin kasar da jihar Filato da wasu sassan Najeriya da aka samu karuwar garkuwa da mutane don kudin fansa da kashe-kashe na baya-bayan nan shi ne kisan wasu sarakunan gargajiya da kuma sace daliban makaranta da malamai a jihar Ekiti.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V
