Ibtila’I! Gobara ta lalata dukiya mai yawa a babbar kasuwar Gusau

FB IMG 1706708856229

Wata gobara ta lalata shaguna da dama a babbar kasuwar Gusau da ke jihar Zamfara inda kuma ta kashe mutum daya.

Alfijir labarai ta rawaito wasu rahotanni sun ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe tara, na daren ranar Litinin a bangaren kayan ɗaki na babbar kasuwar.

Kwamandan hukumar kashe gobara ta Najeriya, Hamza Mohammed, ya sanar da gidan talabijin na Channels cewa wani mai shago wanda har yanzu ba a bayyana sunansa ba ya mutu a lokacin da yake kokarin shiga shagonsa domin kashe gobarar.

Jami’an kashe gobara daga rundunar ‘yan sandan jihar sun yi ta fama da gobarar tun karfe tara na dare. domin hana yaduwar ta zuwa wasu shaguna.

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *