An katse hanyoyin sadarwar wayar hannu a Ƙananan Hukumomin Musawa da Matazu na Jihar Katsina sakamakon ayyukan tsaro da jami’an tsaro ke gudanarwa a yankunan.
Rahotanni sun ce matakin na wucin gadi ne kuma an ɗauke shi domin bai wa jami’an tsaro damar gudanar da ayyukansu cikin sauƙi yayin ci gaba da farautar ’yan bindiga a dazuzzukan yankin.
An bayyana cewa katse hanyoyin sadarwar na daga cikin dabarun da ake amfani da su wajen ƙarfafa ayyukan tsaro da dakile hanyoyin sadarwar masu aikata laifuka.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa za a dawo da sabis ɗin sadarwar da zarar an kammala ayyukan da ake gudanarwa a yankunan.
Haka kuma, an yi kira ga mazauna Musawa da Matazu da su ci gaba da bai wa jami’an tsaro haɗin kai domin tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t