Kotun majistiri mai lamba 6 karkashin mai sharia Umma Kurawa, kotun kuma duba da rashin ladabi da wanda ake kara yayi mata saboda yana daure sai mai Shari’ar ta tashi takanas ta garin nan har zuwa cikin gidan gyaran hali na kurmawar a yau juma’a kotun ta saurari shedar mai kara Mahammad Lawan Rijiyar Zaki Wanda yake karar Sunusi mai nasara da Aliyu Ibrahim Haidar kan zarginsu da hada Kai da zamba cikin aminci da cuta
Tun da farko Sunusi mai Nasara akayi zargin ya siyarwa da Mahammad Lawan gona a kan titin zuwa Karaye ta kimanin miliyan 13, Mahammad Lawan ya bashi miliyan 11 saura miliyan 2 harma sunusi ya bashi takarda ta gona mai dauke da sunan wanda ake kara na biyu Aliyu Ibrahim Haidar inda Sunusi ya shedawa kotu cewa shi daman wakilci yakeyi, ana daf da kammala ciniki wani mutum ya bayyana da cewa gonarsa ce
Bayan sauraren shedar wanda akayi kara na farko Sunusi mai Nasara ya yiwa sheda tambayoyi kan abinda ya fadawa kotu
Lauyan gwamnatin mai gabatar da kara barista Ibrahim Arif Garba ya roki kotu da tayi umarni a kaiwa Aliyu haidar takardar gayyata don ya halarci kotu.
Mai sharia Umma Kurawa tayi umarni a kaiwa Aliyu Ibrahim Haidar takardar gayyata yazo kotu a ranar 30 ga watan da muke ciki domin cigaban sharia
Munyi kokarin ji daga bakin wanda akayi kara Sunusi mai Nasara sai dai lauyansa Barista Ibrahim musa yace suna tattaunawa don samar samar da sulhu a tsakaninsu suna fatan za’a warware
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t