Daga Baba Usman Gama
Dattawan Arewa da na Ibo sun yi alla-wadai da tafiye-tafiyen ShuganaTinubu.
An sace jami’in gwamnati a kusa da sansanin sojin Abuja.
’Yan bindiga sun bukaci N290m da abinci kan mutane 7 suka sace a Abuja.
Musulman Jihar Ondo sun zargi gwamnan jihar da yi masu ƙwauro a rabon muƙaman gwamnati.
Gawarwakin akalla mutane 15 ne aka gano a safiyar Alhamis bayan wani hari a unguwar Ugboju da ke Karamar Hukumar Agatu da ke Binuwe.
Mutane da yawa sun mutu a gobarar da ta tashi a sakamakon rikicin da ya barke tsakanin barayin danyen mai a Jihar Imo.
Rundunar ‘yan sanda ta ce tana neman Rukayya Saadina Dantata ruwa-a-jallo.
Gwamnan Kaduna Uba Sani ya gana da shugaban cin kungiyar yan kasuwar Fanteka da a baya bayan nan ta fuskanci ibtila’in gobara da ta yi sanadiyyar salwantar dukiya mai yawa.
Kotu ta bayar da belin Danbilki Kwamanda.
Ƴan kasuwar Kantin kwari a Kano sun yi addu’a kan matsin rayuwa a Najeriya.
Hukumomi a kasar Saudiyya sun rage kudin aikin Hajji ga maniyyatan da za su sauke farali a 2024.
Kungiyar yan canji a jihar Kano ta ce daga yanzu za ta rika bude kasuwar hada-hadar canji daga karfe 12 na rana zuwa 6 na yammacin kowace rana.
Wata gobara ta kone wata fitacciyar majami’a da ke Legas da aka fi sani da gidan David a lokacin da ma’aikata ke kokarin shirya wa wani taro.
Gwamnatin Bauchi karkashin Bala Muhammed ta musanta hannu a kama Sheikh Dutsen-Tanshi.
Akwai yiwuwar nasara a yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza.
Kamfanin Youtube ya goge tashar da ke wallafa bidiyon marigayi Fasto TB Joshua saboda saba ka’idojin furta kalaman kiyayya.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V
