Hukumar yaƙi da cin hanci ta EFCC ta yi sabuwar fallasa kan masu hannu a harkar satar kuɗaɗen jama’a, Shugaban hukumar, Ola Olukoyede, ya bayyana cewa sun samu wasu ƙungiyoyin addini dumu-dumu a cikin Harkar.
Alfijir labarai ta rawaito Shugaban ya bayyana cewa suna bincikar wata ƙungiyar addini kan zargin taimakawa wajen karkatar da N7bn na kuɗin sata.
Shugaban hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta’annati (EFCC), Ola Olukoyede, ya bayyana cewa hukumar ta gano wasu kuɗaɗe da aka karkatar ta hanyar amfani da wata ƙungiyar addini.
Ola Olukoyede, ya bayyana cewa kuɗaɗen da ake zargin an karkatar ɗin ta hanyar amfani da ƙungiyar addinin sun kai N7bn, cewar rahoton The Punch.
Ya kuma bayyana cewa an gano wata ƙungiyar addini da ke yi wa ƴan ta’adda safarar kuɗaɗe, cewar rahoton jaridar The Nation.
Shugaban na EFCC ya bayyana haka ne a jiya Laraba, a cibiyar Musa Yar’Adua da ke Abuja, yayin wani taro na yini ɗaya kan “matasa, addini da yaƙi da rashawa.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V