Ibtila’I: Yanzu Yan Bindiga Suka Sace Daraktan Hukumar Gidaje a Kusa Da Sansanin Sojoji A Abuja

FB IMG 1706786471509

Wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da Aondo Ver, darakta a hukumar kula da gidajen babban birnin tarayya, Abuja.

Alfijir labarai ta rawaito lamarin ya faru ne a Pambara New Extension dake yankin Bwari ta tsakiya a babban birnin tarayya da misalin karfe 12:30 na daren jiya.

Sabon Extension na Pambara yana da nisan mil 200 daga sansanin sojoji da shingen bincike a Bwari.

An ce masu garkuwa da mutanen sun samu shiga ta shingen tsaron Sojojin sun wuce ta wajen bayan sun yanke wayoyin tsaron

SaharaReporters ta kuma tattaro cewa duk kokarin da ‘yan banga suka yi a yankin na ceto wanda abin ya shafa ya ci tura saboda ba su da makamai.

Sai dai Josephine Adeh, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, ba a samun wayanta har zuwa hada wannan rahoto da SaharaReporters ta yi, an ta ƙoƙarin neman ta amma wayan bata shiga.

A bayan nan ne Jaridar SaharaReporters ta ruwaito yadda wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da wasu ‘yan uwa mata biyu a kauyen Guita, Chikakore a Kubwa, a karamar hukumar Bwari a babban birnin tarayya, Abuja.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *