Ta’adanci! Harin Kunar Bakin Wake Ya Halaka Mutum 24 A Borno

IMG 112634 21625 1750501608313

Rahotanni sun bayyana akalla mutane 24 ne suka rasa rayukansu, yayin da wasu da dama suka jikkata, a wani harin kunar bakin wake da wata mata ta kai a daren Jumma a a garin Konduga, mai nisan kimanin kilomita 36 daga Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta bayyana cewa harin ya auku da misalin karfe 10 na dare a ranar 20 ga Yuni, 2025, a wani wuri da jama’a ke taruwa domin sayen abinci da shakatawa.

Majiyar ‘yan sanda ta sanar da cewa matar yar kunar bakin wake ta tayar da bam din ne a cikin taron jama’a, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 24 da kuma jikkatar wasu da dama, wadanda ba a iya tantance adadinsu ba a yanzu.

“Gawar ‘yar kunar bakin waken ta tarwatse, sai dai an tsinci sassan jikinta, ciki har da kanta, a wurin da fashewar ta auku,” in ji majiyar.

Bayan aukuwar harin, rundunar hadin gwiwa wadda ta haɗa jami’an soji, ‘yan sanda, kwararru kan lalata bama-bamai (EOD-CBRN), sashen leken asiri, JTF na fararen hula (CJTF) da kuma mafarauta, sun kai daukin gaggawa zuwa yankin domin gudanar da bincike da kuma tabbatar da kariyar lafiyar jama’a.

An killace wurin, inda aka gudanar da bincike don gano sauran abubuwan fashewa, amma babu wani abu da aka samu, kamar yadda jami’an tsaro suka tabbatar.

Ha ku zalika an kwashe wadanda suka jikkata zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Maiduguri (UMTH), inda suke karbar kulawa daga likitoci, yayin da aka ajiye gawarwakin wadanda suka mutu a dakin ajiya na asibitin.

A halin yanzu, ana ci gaba da kokarin tantance sunayen wadanda suka mutu da kuma tuntubar iyalansu domin mika gawarwakinsu don gudanar da jana’iza bisa tsarin addini da al’ada.

Rundunar ‘yan sanda ta ce an kara matsa tsaro a Konduga da kewaye domin hana faruwar irin wannan hari a gaba, tare da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *