Wata sabuwar! Manyan jami’an sojin Najeriya 542 sun ajiye aikin su

FB IMG 1750501511658

A ranar Alhamis data gabata ne manyan jami’an sojin ƙasa su 542 suka yi ritaya daga rundunar sojojin Najeriya bayan kammala shekaru 35 suna bauta wa ƙasa.

An gudanar da bikin ritayar a Cibiyar Sake Tsugunar da Sojojin Najeriya da ke Oshodi, Legas. Daga cikin waɗanda suka yi ritayar akwai sojoji 362 daga Rundunar Sojan Kasa, 134 daga Rundunar Sojan Ruwa, da 46 daga Rundunar Sojan Sama.

Da yake jawabi a wajen bikin, Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar Janar Olufemi Oluyede, wanda ya samu wakilcin Manjo Janar Aligbe Obhiozele, ya yabawa sojojin da suka yi ritayar bisa jajircewarsu da kishin ƙasa a lokacin da suke yin aiki.

A cewarsa yau muna yin murnar ƙwazonku, ladabinku da sadaukarwarku wajen hidimar ƙasa. Tafiyarku ta shekaru 35 tana nuna kyawawan halaye na soja kamar jajircewa da ƙaunar ƙasa.

Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835

For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *