Najeriya ta tura sojoji 197 zuwa ƙasar Gambia domin tallafa wa ƙoƙarin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a ƙasar. Wannan mataki na daga cikin gudummawar Najeriya karkashin haɗin gwiwar ƙasashen ECOWAS wajen tabbatar da zaman lafiya a yammacin Afirka.
Sojojin da aka tura sun haɗa da kwararrun dakarun rundunar sojin kasa (NA), sojin ruwa (NN), da sauran hukumomin tsaro. An shirya aikin ne domin tallafa wa gwamnatin Gambiya wajen tabbatar da doka da oda, da kuma hana yaduwar rikice-rikicen cikin gida da na makwabta.
Wannan na zuwa ne a wani lokaci da ƙasashen yammacin Afirka ke fuskantar ƙalubalen tsaro, ciki har da juyin mulki, ƙungiyoyin masu tayar da kayar baya da kuma rikice-rikicen siyasa.
A cewar jami’an tsaro, an yi cikakken atisaye da horarwa kafin tura dakarun, kuma an tabbatar da cewa za su aiwatar da aikin cikin kwarewa da biyayya ga ƙa’idojin ƙasa da na duniya.
Najeriya dai na daga cikin manyan masu ruwa da tsaki a harkokin zaman lafiya a nahiyar Afirka, musamman ta fuskar bayar da gudummawa ga ayyukan ECOWAS da AU (Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka).
Domin bada talla ko shawarwari a iya kiranmu a wannan lambar +2348032077835
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news fallow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD