Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da sauke Dr. Nasiru Yusuf Gawuna daga matsayin Shugaban Majalisar Gudanarwa (Pro-Chancellor) na Jami’ar Bayero, Kano (BUK), tare da naɗa Air Vice Marshal (AVM) Sadiq Ismaila Kaita (mai ritaya) a matsayin wanda zai gaje shi.
Sanarwar da mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru, Mr. Bayo Onanuga, ya fitar ranar Juma’a, ta bayyana cewa an sauke Dr. Gawuna ne domin ya mai da hankali kacokan kan aikinsa na Shugaban Hukumar Gidaje ta Ƙasa (FHA), wacce ke ƙarƙashin Ma’aikatar Gidaje da Ci Gaban Birane.
“Shugaban Ƙasa ya yanke wannan hukunci ne domin ba Dr. Gawuna damar mai da hankali kan aikin da ke gabansa a FHA,” in ji sanarwar.
AVM Sadiq Kaita (mai ritaya) tsohon jami’in rundunar sojin sama ne, wanda ya riƙe muƙamai da dama a matakin ƙasa.
Ciki har da Darakta na Tsare-tsare a Hedikwatar Tsaro da kuma Shugaban Sashen Sauya Tsari da Ƙirƙira a Fannin Tsaro.
Tarihin aikinsa ya haɗa da ƙwarewa wajen tsara manufofi, gyaran tsare-tsare da kuma horar da jami’an tsaro.
Ana sa ran zai kawo irin wannan gogewa a shugabancin majalisar jami’ar, musamman a lokacin da jami’o’in Najeriya ke fuskantar ƙalubale da dama, ciki har da ƙarancin kayan aiki da gasa a matakin duniya.
Jami’ar Bayero na daga cikin manyan cibiyoyin ilimi a Arewacin Najeriya, wacce ke taka muhimmiyar rawa a fannin bincike, ilimi da samar da mafita ga manufofin ci gaban ƙasa.
Sauke Dr. Gawuna daga wannan muƙami ya biyo bayan damuwar da ke tattare da rike manyan muƙamai biyu lokaci guda na FHA da BUK abin da ka iya kawo cikas ga gudanar da ayyuka yadda ya kamata.
Dr. Gawuna, wanda ya taɓa rike muƙamin mataimakin gwamnan Jihar Kano da kuma ɗan takarar gwamna a jam’iyyar APC, na da dogon tarihi a harkokin mulki.
Yanzu ana sa ran zai mai da hankali kan sabbin ayyukansa a hukumar FHA, musamman ganin matsayin da hukumar ke da shi a shirin samar da gidaje masu araha na gwamnatin Tinubu.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t