
Alfijr ta rawaito Saudi ta baiwa Nijeriya kason kujeru dubu arba in da uku 43 domin zuwa aikin Hajjin 2022.

Muhammad Abba Dambatta wanda shine Babban Sakataren Hukumar Jin daɗin Alhazai na Kano, shine ya sanar da hakan yayin taron manema Labarai a yau Laraba.
Ya kara da cewa, hakan ya biyo bayan yadda kasar Saudiyya ta ce adadin mutune Milyan daya ne kadai za su gudanar da aikin Hajjin na bana a fadin duniya, wannan adadi da aka baiwa Najeria na da alaka da yawan mutanen da Najeria ta ke da shi.
Alfijr
Babban Sakataren ya ce, ko da ya ke har yanzu hukumar NAHCON ba ta fitar da adadin kudin aikin hajjin bana ba, alamu na nuna cewa kudin zai ƙaru fiye da yadda aka biya a shekarun baya
Ya ce a baya an canja Dalar Amurka akan naira 350, yanzu kuma ta kai N408, in da hakan ke nuna lallai za a samu ƙarin kudin.