Daga Rabiu Usman
Rundunar ‘yan sintiri ta vigilantee a jihar kano ta shirya tsaf domin daukar kwararan matakan tsaro na kare rayuka da dukiyoyin Al’ummar jihar kano domin tunkarar duk wani mutum ko kungiyar da ke shirin yin amfani da al’adar yin tashe a bana don aikata wani mummunan laifi na kwacen waya ko haura gidajen mutane da kuma yin fashi da makami.
Alfijir labarai ta rawaito babban kwamandan vigilantee na jihar, Alhaji Shehu Rabiu ne ya bayyana hakan a yau yayin ganawar sa da manema labarai a Babbar shalkwatar rundunar dake zaman ta a unguwar hotoro.
Ya ce yanda ake aikata laifuka a fadin jihar sakamakon irin wannan Al’adar ta tashe a kowacce shekara, yanzu haka sunyi dogon nazari akan yawaitar laifukan wanda kuma yanzu an gano cewa wasu matasa na shirin yin amfani da Tashen don aikata miyagun laifukan da zasu shafi al’umma kai tsaye.
Wanda yace tuni dai jami’an vigilantee a farin kaya da kuma na kayan sarki suka bazama loko da sako a fadin jihar domin gano Sirrin yanda bata garin suke shiryawa domin ɗaukar matakin gaggawa.
Ya kara da cewar, tuni jami’an vigilantee suka haɗa kai da rundunar yan sandan kano domin dakile afkuwar aikata laifukan daba daban daban a faɗin jihar kano da kuma mika su ga hukumar data dace don ɗaukar matakin da ya dace dasu.
Ya kara da cewar, duk wanda suka kama babu shakka zai fuskanci fushin hukuma domin zasu dangana dashi kotu domin zartar da hukuncin da ya dace da shi.
Wakilin mu ya ruwaito cewar, a ƙarshe kwamandan yayi kira ga iyaye dasu dinga sanya idanu akan duk wani motsin yaran su domin gudun fadawa hannun wasu bata garin matasa masu aikata manyan laifukan daba da shaye shayen miyagun kwayoyi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk