Labari Mai Dadi! Kamfanin Dangote Ya Fara Ciyar Da Mutane Dubu 10 A Kano Da Kuma Raba Shinkafa Buhu Miliyan 1 A Najeriya

IMG 20240318 WA0154

Dangote na ciyar da mutane 10,000 a Kano kowace rana albarkacin watan Ramadan, ya kuma raba buhunan shinkafa miliyan 1 a fadin kasar.

Alfijir labarai ta rawaito Attajirin da ya fi kowa kudi a Afirka, Alhaji Aliko Dangote, ta hannun gidauniyarsa Dangote foundation ya kaddamar da rabon abinci kyauta ga al’ummar Musulmin da ba su wuce 10,000 ba a jihar Kano, jiharsa ta asali a kullum.

Gidauniyar ta kara wa’adin ne domin raba buhunan shinkafa miliyan daya da kudinsu ya haura Naira biliyan 13 a fadin jihohi 36 na tarayya da Abuja domin rage radadin yunwa a kasar.

Manufar ita ce a sassauta wa miliyoyin ‘yan Najeriya wahala a cikin kalubalen tattalin arzikin da Kasar ke ciki.

Gidauniyar bata tsaya nan ba kawai, ga rabon biredi 20,000 a kullum ga mazauna Kano da kuma 15,000 a kullum ga mazauna jihar Lagas, wanda an fara wannan tago mashin alherin ne tun Shekarar 2020 a lokacin COVID, wanda Allah ya bada ikon ci gaba har kawo yanzu.

Ire-iren abincin da ake dafawa na Ramadan kyauta ya hada da jollof rice, farar shinkafa da stew, jollof spaghetti, wake da kaza da naman sa, sannan kuma a hada da ruwan sha ga kowane mutum.

IMG 20240318 WA0153
📸 Dangote

Ana raba abincin ne a masallatan Juma’a da tituna da gidajen gyaran hali da gidajen marayu da sauran wurare a cikin birnin Kano da kewaye.

Wani wanda ya ci gajiyar abincin mai suna Musa Maikatako mazaunin unguwar Tarauni a tattaunawarsa da Jaridar Alfijir Labarai ya nuna jin dadinsa da wannan karimcin da aka yi masa, ya kara da cewar an taimaka masa wajen yin buda baki don zuwa lokacin da aka bashi wannan tallafin bashi da abin da zai yi bude bakin, wannan tallafi yana taimakon alumma da dama Musamman wannan yanayi da ake ciki, duba da halin da ake ciki a kasar nan. Don haka dole mu godewa Allah tare da wannan kamfani na Dangote, duba irin wannan kabakin arzikin da yake saukewa al’umma.

Hakazalika wata wadda ta ci gajiyar tallafin, Hajiya Inna Tukur, ta bayyana jin dadin ta da wannan rabon abincin, wanda a cewarta Gidauniyar Aliko Dangote ta kawo mata dauki, wanda da badon su ba da sun shiga wani hali, don haka muna cikin farin ciki da wannan kamfanin.

“Ba abin da zan ce sai dai in yi godiya ga Allah sannan da Alhaji Aliko Dangote, ina rokon Allah Ya kara muku albarka a al amuranku.”

Gidauniyar Aliko Dangote yanzu haka ta kai shekaru hudu tana rabon biredi ga Al umma kyauta, sannan an shafe sama da shekaru 30 ana ci gaba da ciyar da mabukata a Kano domin sanya farin ciki da Alhaji Aliko Dangote ya kuduri aniyar yi.

Ana gudanar da wannan hidimar ne daga gidan mahaifiyar sa Hajiya Mariya Sunusi Dantata da ke unguwar Koki da kuma wuraren dafa abinci daban-daban. Wannan shirin ciyarwa yana Isa ga mazauna Kano Mutum 10,000 a kullum kama da karin kumallo, abincin rana, da kuma abincin dare.

IMG 20240318 WA0152
📸 Dangote
IMG 20240318 WA0155
📸 Dangote
IMG 20240318 WA0156
📸Dangote

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *