Alfijr ta rawaito Gobara ta kone hedkwatar tsaro a Abuja Hedikwatar tsaro da ke Abuja,
lamarin dai ya shafi hawa na biyu na ginin.
Har yanzu dai ba a san musabbabin tashin gobarar da ta faru a ranar Litinin ba har lokacin hada wannan rahoto.
Daraktan yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Jimmy Akpor, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya bayyana cewa an shawo kan lamarin.
Ya ce an shawo kan lamarin ne sakamakon hadin gwiwa da sojoji da jami’an hukumar kashe gobara ta tarayya suka yi.
“An kuma kwashe dukkan ma’aikata da suke cikin hawan ba tare da jikkata ko rasa rai ba.
An fara gudanar da bincike don gano musabbabin tashin gobarar nan take.
“Muna godiya ga hukumar kashe gobara ta tarayya da sauran jama’a saboda ci gaba da goyon baya da fatan alheri ga rundunar sojojin Najeriya,” inji shi.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇