Takaita Cirar kudi, ‘Yan Siyasa Zaifi shafa ba Talakawa Ba. Sanusi ll

Daga

Aminu Bala Madobi

Alfijr ta rawaito Tsohon Sarkin Kano na 14, Kuma masanin tattalin arziki, Khalifa Muhammad Sanusi ll ya ce matakin da babban bankin Najeriya ya dauka na takaita cirar kudade yau da kullum zai fi yin tasiri kan `yan siyasa ba talakawa ba.

Sanusi ll ya bayyana haka ne a karshen karatun da yake gabatarwa na Madarijus salikeen da ya saba yi duk karshen mako.

Ya ce `yan siyasar kasar na amfani da kudi a lokacin zabe don sayen kuri’un jama’a, lamarin da ke haifar da koma-baya ga cigaban kasar.

Muhammadu Sanusi na II ya ce “abin takaici ne yadda mutane za su yi shekara hudu suna kwasar dukiyar mutane kuma, suna barin mutane a cikin wahala, fatara da yunwa, sannan su fito da irin kudaden dasuka boye domin su sayi kuri’u, su biya ‘yan sanda, da DSS, da ma’aikatan INEC da `yan daba a sayo musu kwaya, a saya musu makamai, don hana mutane zabe.”

Daganan tsohon Sarkin na Kanon ya ce wannan tsari da bankin CBN ya fito da shi, shi ne zai fara rage barnar da ‘yan siyasa ke yi kuma zai takaita tasirin magudin zabe a tarihin Najeriya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

One Reply to “Takaita Cirar kudi, ‘Yan Siyasa Zaifi shafa ba Talakawa Ba. Sanusi ll”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *