
Alfijr ta rawaito ,Majalissar masarautar Gumel ta bayyana ranekun gudanar da sallar Gani ta bana
Alfijr Labarai
Sakataren Majalissar kuma Majidadin Gumel, Alhaji Murtala Aliyu ya tabbatar da hakan ga wakilin Gidan Radio jigawa
Yace za a gudanar da bukukuwan sallar Ganin ne a ranekun Juma-a da Asabar da kuma Lahadi, 7 da 8 da kuma 9 ga watan gobe idan Allah ya kaimu
Alhaji Murtala Aliyu ya kara da cewar tuni aka sanar da hakimai da Dagatai da masu unguwanni domin yin shirin gudanar da bikin na Gani na bana.
Alfijr Labarai
Majidadin na Gumel ya cigaba da cewar an gayyato muhimman mutane da suka hadar da sarakuna da sauran masu mukaman gargajiya domin kara kawata bikin.