Takaitattun Labaran Duniya Na Safiyar Alhamis 14/06/1445 – 28/12/2023

best seller i2

Daga Baba Usman Gama

Kotu a Jihar Kano ta tisa keyar wata matar auren da ake zargi da kisan ma’aikacin gidanta mai suna Nafiu Hafiz Gorondo zuwa gidan yari.

Sabon gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya fara da nada sabbin mukamai.

Adadin mutanen da aka kashe a jihar Filato ya karu zuwa kusan 200, kamar yadda hukumomi suka bayyana a yayin da aka soma binne wadanda suka mutu.

Ambaliya ta kashe mutum 40 a Jamhuriyar Congo.

Kamfanin jiragen ruwan Faransa ya koma anfani da mashigar tekun Bahar Maliya.

Kotu ta wanke Trump don bashi damar shiga takarar fidda gwani.

Iran da Rasha sun kulla yarjejeniyar kasuwanci da kudadensu maimakon dalar Amurka.

Safarar mutane: Indiya na binciken yadda wasu ‘yan kasarta suka fada wani jirgi da Faransa ta tsare.

‘Yan sanda a Kenya na binciken kisan mutane da aka yi a wata gonar abarba.

Rasha ta yi kira da a kawo karshen zaluncin da Falasdinu ke fuskanta a tarihi.

EPL: Manchester City ta sami nasara akan Everton da ci 3:1 a wasan jiya.

EPL: Chelsea ta sami nasara akan Crystal Palace da ci 2:1 a wasan jiya.

EPL: Wolves ta sami nasara akan Brentford da ci 4:1 a wasan jiya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *