Daga Baba Usman Gama
Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya kaddamar da katafaren ginin ofishin Gwamnan Kano da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi wa kwaskwarima a cikin gidan gwamnatin jihar.
’Yan sanda da mafarauta sun aika ’yan bindiga 6 lahira bayan wani artabu a Karamar Hukumar Ningi ta Jihar Bauchi.
Rundunar ƴan sanda a jihar Imo ta tabbatar da mutuwar wani jami’inta sakamakon harbin da da budurwarsa ta yi masa.
Ƴan sanda na neman waɗanda suka yi wa wani yaro dan shekara 8 mummunan kisan gilla a Zariya jihar Kaduna.
Babbar Kotun jihar Kano ta dakatar da shugaban karamar hukumar Gwale Khalid Ishaq Diso daga alakanta kansa a matsayin shugaban rikon karamar hukumar.
Gwamnan Jigawa, Umar Namadi ya sanya hannu kan kasafin kudin jihar na 2024 da ya kai Naira biliyan 298.
Wani soja ya kashe direban motar kayan agaji saboda kin ba shi na-goro a hanyar Dikwa zuwa Gamboru da ke Jihar Borno.
Ana makokin kwana uku a Ondo kan mutuwar Akeredolu.
Hukumar kula da kare hakkin masu saye da sayarwa a Najeriya ta umarci kamfanin sigari na British American Tobacco da ya biya tarar dala miliyan 110.
Kasar Benin ta janye dakatar da shigar da kayayyaki zuwa kasar Nijar.
Jagoran RSF na ziyara a Habasha da Uganda don sasanta rikicin Sudan.
Rasha ta sake bude ofishin jakadanci a Burkina Faso bayan shekaru 32 da kullewa.
Wata fashewa bayan hadarin tankar dakon gas ta kashe mutane 40 a Liberia.
‘Yan sandan Congo sun tarwatsa masu zanga-zangar adawa da sakamakon zabe.
Ambaliya ta kashe mutum 40 a Jamhuriyar Congo.
Dubban matasan Isra’ila sun yi maci don buƙatar sakin ƴan ƙasar da ake garkuwa da su.
An kai harin rokoki a garuruwan kudancin Isra’ila.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IUuk7jeH4yvAkwOmbOCSfl