Kwamishinan yan sanda Ya garkame yan sanda 3, bisa zargin karbar na goro

FB IMG 1717108061650

Daga Aminu Bala Madobi

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Anambra, Ikioye Orutugu, ya bayar da umarnin tsare wasu ‘yan sanda uku masu mukamin sufeta bisa zargin cin hanci da rashawa.

Rahotonni Sun tabbatar da cewa ’yan sandan sun tsare wasu jama’a da ba a san ko su wanene ba a lokacin da jami’an tsaro ke sintiri, inda suka yi ta bincike a wayarsa ta karfim tsiya.

A cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a ranar Laraba, mai magana da yawun rundunar, Tochukwu Ikenga, ya ce biyo bayan shigarsu cikin laifin da ake zargin, Kwamishinan Yansandan ya ba da umarnin a ladabtar dasu cikin gaggawa.

Sanarwar ta kara da cewa, “Kwamishanan ‘yan sandan jihar Anambra, Ikioye Orutugu, a ranar 11 ga watan Yuni, 2025, ya bayar da umarnin tsare sufeto ‘yan sanda uku bisa zargin cin hanci da rashawa.

“Ya kuma ba da umarnin a gaggauta gurfanar dasu don ladabtar dasu.

“Kwamishinan, a lokacin da yake yi wa Jami’an tambayoyi, ya fusata ayayin baje kolin yadda suka yi wa wani mutum da ba a san ko wanene ba, a lokacin da jami’an tsaro ke sintiri, suka binciko wayarsa da karfi, sannan suka kwace daga hannun wanda abin ya shafa.

“Kwamishinan daga nan ya jaddada cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya, a matsayinta na mai da’a, mai gaskiya, mai rikon amana, mai bin doka da oda, ba za ta lamunci irin wannan cin fuska da cin zarafin ofis, cin hanci da rashawa da kuma rashin sanin makamar aiki ba.”

Ga Masu Son Bada Talla A Kira   +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *