Editor
Mahalarta taron ASCON anan kano sun yaba da yadda masu ruwa da tsaki na Hukumar ASCON bisa zakulo ƙwararru kuma gogaggun masana domin horas da su don inganta ƙwarewarsu.
Taron bitar na makonni biyu dake gudana anan kano, Rukunin ma’aikatan da ke a matakin albashi na 13 zuwa 14, sun jinjina tare da nuna gamsuwa la’akari da irin horo da kulawa ta musamman da jami’an Ascon ke musu cikin nutsuwa da nuna kwarewa.
Taron horaswar karo na 25, an shirya shine a dakin taro na State Library domin kara musu dabarun kwarewa da sanin yadda ake gudanar da ayyukan gwamnati (Administration).
Da take jawabi a madadin Darakta Janar na ASCON, Mataimakiyar Daraktar Sashen Horaswa, Uwargida A.O. Olabimitan, ta yaba da jajircewa, natsuwa da biyayyar da mahalarta bitar suka nuna ayayin da ake cigaba da bitar horaswar ta tsawon makonni biyu. Ta kuma ce irin wannan himma da ma’aikatan suka nuna abin a yaba ce
Tunda fari datake jawabi shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Hajiya Bilkisu Shehu Mai-Mota, ta bayyana cewa an tsara taron ne domin gina ƙwararrun ma’aikata masu nagarta, gaskiya da riƙon amana. Ta kuma yabawa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa yadda yake ci gaba da bai wa horarwa da sake horas da ma’aikata muhimmanci, tare da ɗaukar ƙwararrun ma’aikata domin ƙarfafa aikin gwamnati.
Yayin gabatar da muhimmin jawabi, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, wanda Sakataren Gwamnatin Jihar Kano ya wakilta, ya sake tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da tallafa wa shirye-shiryen horas da ma’aikata domin inganta ƙwarewa, ƙarfafa aikin gwamnati da samar da ingantaccen hidima ga al’umma. Ya ce gwamnatin sa ba za ta gajiya ba wajen ƙarfafa cibiyoyin gwamnati da samar da ma’aikatan da za su taka rawar gani wajen ci gaban tattalin arziki da zamantakewar Jihar Kano.
Ɗaya daga cikin mahalarta taron, Musa Ibrahim Ahmad, (Best seller) ya bayyana farin cikinsa kan yadda aka gudanar da horaswar.
“A gaskiya muna matuƙar godiya ga kwamitin shirya taron ASCON saboda yadda suka zaɓo ƙwararru da gogaggun masana waɗanda suke ba mu ilimi a tsawon wannan horaswa.
“Babu abin da za mu ce wa jami’an ASCON face godiya da fatan alheri.”
Ya ƙara da cewa: “Muna kuma miƙa godiya ta musamman ga Mai Girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, saboda dawo mana da wannan muhimmiyar damar samun irin wannan horaswa, wadda gwamnatocin baya suka yi watsi da ita.”
Musa Best Seller ya kuma yabawa Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Kano, Hajiya Bilkisu Shehu Mai-Mota, bisa irin jagoranci nagari da tsayawa tsayin daka da ta yi wajen tabbatar da cewa an gudanar da taron cikin tsari, nasara da inganci.
Hajiya Hassana Aliyu ita ma na daya daga cikin mahalarta wannan horaswar ta bayyana cewar a gaskiya babu abinda zamu ce da Ascon musamman jarorar wannan tawagar wato Uwargida A.O. Olabimitan Mataimakiyar Daraktar Sashen Horaswa ta hukumar Ascon din sai godiya da fatan alheri, saboda jajircewarta kan lalle sai mun fahimci abinda ake koya mana, babu shakka “kwalliya ta biya kuɗin sabulu.”
Allah ya taimaki gwamnatin Kano da shugabar ma’aikatan jihar Kano ameen
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t