Kotun Koli a yau Laraba ta kawo ƙarshen kusan shekaru goma sha tara na shari’a kan kujerar sarautar Gwandu, inda ta soke hukuncin da ya dawo da Al-Mustapha Haruna Jokolo a matsayin Sarkin Gwandu na 19.
A cikin hukuncin da Mai Shari’a Emmanuel Agim ya karanta, kotun kolin ta yanke cewa Babbar Kotun Jihar Kebbi ba ta da hurumin sauraron ƙarar da Jokolo ya shigar, saboda bai bi hanyoyin sasanta rikici da dokar nadawa da sauke sarakuna ta Jihar Kebbi ta tanada ba.
Kotun ta bayyana cewa a ƙarƙashin Sashe na 5(4) na dokar, duk wanda ke da ƙorafi ya kamata ya fara miƙa ƙararsa ga Gwamnan Jihar Kebbi kafin ya nemi taimakon kotu.
“An shigar da wannan ƙara kafin cika sharudan doka, musamman buƙatar gabatar da ƙorafi ga gwamna. Saboda haka, kotun farko ba ta da hurumi, kuma hukuncinta ya zama babu amfani,” in ji Mai Shari’a Agim.
Ga Masu Son Bada Talla A Kira +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zN