Kotu Ta Yankewa shaharariyar yar Tiktok Murja Kunya Hukuncin Daurin Watanni Shida a Kano

FB IMG 1748465563488

Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta yankewa jarumar TikTok, Murja Ibrahim Kunya (Yagamen), hukuncin zaman gidan yari na tsawon watanni shida ko kuma zabin biyan tarar naira dubu hamsin (₦50,000.00),  sakamakon samunta da laifin wulalanta takardun kudi na Najeriya (Naira).

Alkalin kotun ya yanke wannan hukunci ne bayan sauraron shari’ar da aka shigar kan Murja bisa karya dokar da ta haramta lalata ko wulakanta takardun kudi a karkashin kundin tsarin mulkin Najeriya.

Baya ga hukuncin tarar ko dauri, kotun ta kuma umarci Murja da ta zama jakadiya ga Babban Bankin Najeriya (CBN) da Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) domin taimakawa wajen wayar da kan al’umma game da illolin da ke tattare da lalata ko wulakanta kudi.

Wannan hukunci na zuwa ne a wani bangare na kokarin hukumomi na dakile lalata ko wulakanta naira, da ke yaduwa musamman a lokutan biki ko shagulgula, wadda ke rage darajar takardun kudi da kuma kara wa gwamnati nauyi wajen sake buga sababbin kudade.

Hukumomin CBN da EFCC sun jaddada cewa duk wanda aka kama da laifin lalata ko wulakanta naira zai fuskanci hukunci mai tsanani, domin dakile wannan dabi’a da ke barazana ga tsaron kudi da tattalin arzikin kasa.

An shawarci jama’a da su kiyaye amfani da kudi cikin mutunci da daraja, tare da taimakawa hukumomi wajen ganin an dakatar da irin wannan karya doka.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *