Kotu ta ba da umarnin ƙwace kadarorin tsohon Ministan wutar lantarki, Saleh Mamman tare da  umartarsa  da ya mayar da biliyan 22

FB IMG 1783437393407

Babbar kotun tarayya da ke Maitama a Abuja ta ba da umarnin ƙwace wasu kadarori biyar mallakin tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, wanda ke zaman hukuncin daurin shekara 75 bisa laifukan cin hanci da rashawa.

Alƙali James Omotosho ya bayar da umarnin ne a ranar 2 ga Yuli, inda ya amince da ƙwace ginin Walijam Apartments da ke Wuse 2, Abuja har abada, bayan ya yanke cewa hukumar EFCC ta tabbatar an saye shi da kuɗaɗen da aka samu ta haramtacciyar hanya.

Sauran kadarori huɗu da kotun ta bayar da umarnin ƙwace su na wucin gadi sun haɗa da Bloom Luxury Suites Nigeria Limited da ke Kaduna, wasu gidaje biyu da ke titin Misratah a Wuse 2, Abuja, da kuma A.U.A Plaza da ke Kade Street, Wuse 2.

Kotun ta kuma umarci EFCC da ta wallafa sanarwar ƙwace kadarorin na wucin gadi a wata jarida ta ƙasa cikin kwanaki bakwai domin bai wa duk mai da’awa damar gabatar da hujjar da za ta hana a ƙwace su gaba ɗaya.

Tun da farko, EFCC ta gurfanar da Saleh Mamman kan tuhume-tuhume 12 da suka shafi cin hanci da halasta kuɗaɗen haram da darajarsu ta kai Naira biliyan 33.8. Kotun ta same shi da laifi a dukkan tuhume-tuhumen tare da yanke masa hukuncin ɗaurin shekara 75.

Haka kuma, kotun ta umarce shi da ya mayar da Naira biliyan 22 da EFCC ta gano suna da alaƙa da laifukan da aka same shi da su.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *