Gwamnatin Najeriya za ta binciki kamfanonin sada zumunta na Meta, X da AI

FB IMG 1723115651747

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta gudanar da bincike kan manyan kamfanonin fasaha na duniya da suka haɗa da Meta, X (Twitter), Alphabet da kuma wasu kamfanonin fasahar AI da ke aiki a Najeriya.

Hukumar kare haƙƙin masu amfani (FCCPC) ta ce binciken ya biyo bayan zarge-zargen karya dokokin amfani da ɗaukar bayanai daga kafafen yaɗa labarai ba tare da izini ba, da kuma wasu mu’amaloli da ake ganin na iya zama rashin adalci ga tsarin dijital a ƙasar.

Matakin ya biyo bayan umarnin da shugaban ƙasar, Bola Ahmed Tinubu, ya bayar ga hukumar FCCPC, domin ta duba wani korafi da ƙungiyar masu yaɗa labarai ta Najeriya, NPO ta gabatar wa fadar shugaban ƙasa.

Binciken zai mayar da hankali kan zargin cewa kamfanonin sun naɗi bahanai ko sun yi amfani da labarai da sauran bayanan kafafen yaɗa labarai na Najeriya wajen horar da fasahar AI ba tare da izinin hukumomi ba.

Ƙungiyar NPO ta ce ta damu kan “yadda kamfanoni irin su Meta, Alphabet, X da wasu AI ke amfani da labarai ba tare da izini ko haƙƙin mallaka ba, wanda hakan ke rage samun kuɗaɗen shiga ga kafofin.”

Mataimakin shugaban FCCPC Mr. Tunji Bello, ya ce hukumar za ta gudanar da bincike na gaskiya bisa hujjoji, tare da tabbatar da cewa dukkan ɓangarori za su samu damar bayyana matsayarsu.

Ministan yaɗa labarai da wayar da kai na ƙasar, Mohammed Idris, ya miƙa umarnin a wata takarda da yasanya wa hannu.

FCCPC ta taɓa gudanar da bincike kan Meta a shekarar 2025, inda ta ci kamfanin tarar dala miliyan 220 bisa zargin karya dokokin kariyar bayanai, duk da cewa kamfanin ya ɗaukaka ƙara kan hukuncin.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *