Wata kotu dake zamanta a garin Kano ta yi umarnin kulle asusun bankunan hukumar Hisba bisa gurfanar da ita da wasu masu Hotel-hotel suka yi a gaban kotun.
Alfijir labarai ta rawaito lokacin da yake tabbatar da faruwar hakan a zantawarsa da TRT Africa, babbab kwamandan hukumar ta Husbar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya ce kawo yanzu ba’a sanar da su laifin da suka aikata ba har aka dauki matakin rufe asusun bankunan nasu.
Sheikh Aminu Daurawa ya kuma ce sun san dai an aika musu da wata takardar kotu da take nuni da cewar, akwai wani Hotel da suka taba zuwa aiki wanda suka ce sai sun biya Naira dubu dari bakwai, da kuma wani daban wanda shi ma suka taba zuwa aiki, shi ma zasu biya dubu dari a lokacin.
Daurawa ya ce kamata ya yi a fada musu laifin da suka aikata domin su nemi lauya ya shiga cikin batun wanda idan suka kasa kare kansu sai ayi musu hukunci.
Kwamandan Hisban ta Kano ya ce matakin da aka dauka din yanzu haka ya dakatar da ayyukansu kasancewar ba zasu iya taba kudaden asusun su ba.
Ya Kara da cewar yanzu haka ya tura wakili domin yaje ya samu kwamishinan shari’a na jihar Kano, kuma babban lauyan gwamnati Barista Isah Haruna Dederi, domin ba’a sanar musu dalilin daukar matakin rufe asusun bankunan nasu ba.
Idan dai ba’a manta ba a kwanakin baya ne hukumar Hisbar ta jihar Kano, ta rinka kai sumame a Hoto-Hotel, da guraren shakatawa a jihar inda ta rinka kama mutane, da tayi wa take da Operation kau da Badala, lamarin da ya rinka janyo cece-kuce a lokacin
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V