Ministan sufurin jiragen sama da raya sararin samaniya, Festus Keyamo, a yau Laraba, ya bayyana cewa hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC, na binciken cece-kucen da ake tafkawa a kan cinikin jiragen Najeriya da tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika ya kulla.
Alfijir labarai ta rawaito Sirika ya kasance ministar sufurin jiragen sama a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari
Ministan ya bayyana hakan ne a cikin shirin Siyasa a Yau na Channels Television.
Ya ce, “Hukumar EFCC na binciken wannan yarjejeniya. Ana ci gaba da binciken laifukan da ake zargin tsohon ministan ya tafka.”
Idan zaku tuna a watan Mayu Alfijir labarai ta wallafa cewa jirgin da shugaba Buhari ya kaddamar a lokacinsa kwanaki kadan kafin ya bar mulki, ya haura shekaru 10 a duniya kuma mallakin kamfanin jiragen sama na Ethiopia ne.
Plane Spotters, wani dandali wanda ke ɗaukar lissafin jiragen sama, ya bayyana Yanayin sa S Q4005C kuma Serial Number shine 40965/4075.
Ministan sufurin jiragen sama na yanzu ya kuma bayyana cewa gwamnatin Tinubu ba ta da wani shiri na maida wani kamfanin jiragen sama na cikin gida ya zama kamfanin jigilar kayayyaki na kasa.
Ya ci gaba da cewa: “Za mu kafa kamfanin jigilar kayayyaki na kasa daban.”
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V