Kamfanonin Mai Na Dangote Ya Magantu Akan Maganar Farashin A Najeriya

FB IMG 1722187869789

Wata sanarwar ta yi kira ga ‘yan ƙasar su yi watsi da rahoton da ya ambato ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN) tana cewa hamshaƙin attajirin zai riƙa sayar da kowace lita ɗaya ta fetur a kan N600.

Alfijir labarai ta ruwaito mai magana da yawun kamfanonin Dangote, Anthony Chiejina, ya fitar ranar Talata ta yi kira ga ‘yan ƙasar su yi watsi da rahoton da ya ambato ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN) tana cewa hamshaƙin attajirin zai riƙa sayar da kowace lita ɗaya ta fetur a kan N600.

“Muna so mu yi bayyana cewa ƙungiyar dillalan man fetur ta Nijeriya (IPMAN) ba ƙawar kasuwancinmu ba ce kawo yanzu. Ba mu taɓa tattaunawa da ita ba a game da farashin man fetur, kuma ba ta da iko ko hurumin yin magana a madadinmu, mai daɗi ko mai tattare da ɓoyayyiyar manufa,” in ji sanarwar.

Matatar man fetur dinmu za ta samar da dubban ayyuka ga matasa – Dangote

“Muna kira ga al’umma su guji watsa jita-jita. Muna da hanyoyin isar da saƙonninmu waɗanda masu ruwa da tsaki suka sani.”

Kamfanin Dangote ya fitar da sanarwar ce a daidai lokacin da ya sha alwashin soma sayar da man fetur a watan nan na Agusta, kamar yadda Anthony Chiejina ya shaida wa manema labarai.

A baya, kamfanin ya sanar da cewa zai soma sayar da fetur a watan Yuli, sai dai ya jinkirta soma yin hakan saboda wasu dalilai da suka haɗa da tashin gobara a wani ɓangare na kamfanin, kamar yadda attijiri Aliko Dangote ya bayyana.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *