Daga Aminu Bala Madobi
Dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar mazabar Gudu, Yahaya Gudu, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.
Alfijir ta rawaito wasu ‘yan ta’adda sun kashe wani sabon aure jami’in sojan Najeriya Ibrahim Yibranii Yohana da wasu sojoji uku a jihar Sokoto.
‘Yan ta’addan sun kashe sojoji hudu ne a lokacin da suka yi musu kwanton bauna akan hanyar Kukurau-Bangi, a karamar hukumar Gudu da ke jihar da misalin karfe 4:00 na yammaci.
An kuma ce harin ya yi sanadin jikkata wasu sojoji biyu. ‘Yan ta’addar sun kona motocin jami’an sojojin da ke aiki guda biyu.
Dan majalisar dokokin jihar Sokoto mai wakiltar mazabar Gudu, Yahaya Gudu, ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin.
Wani da ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, ya ce ‘yan ta’addan sun kuma kona motocin sintiri na sojojin guda biyu.
“Eh, gaskiya ne. Wasu ‘yan bindiga sun yi wa sojoji da ke sintiri kwanton bauna a kan hanyar Kukurau-Bangi inda suka kashe hudu daga cikinsu yayin da wasu biyu suka jikkata.
“Sun kuma kona motocin sintiri na sojojin,” in ji dan majalisar.
Ya ce an sanar da Gwamna Ahmed Aliyu game da harin, kuma an aika da wani karin taimako zuwa yankin a wannan rana.
Wani mazaunin garin Gudu wanda ya shaida wa Aminiya cewa, an ga ‘yan ta’addan suna kaikomo a yankin a kan babura kusan 20.
Ya ce: “Kowanne babur na dauke da ‘yan fashi biyu dauke da muggan makamai. Ba su taɓa ko sace kowa a cikin al’ummarmu ba. Sun wuce kawai kuma abin da muka ji shi ne karar harbe-harbe.
“Su ’yan ta’adda har yanzu suna cikin wannan daji. Akwai rafi da suke haduwa ana tattaunawa kowacce rana.
Mun sha gaya wa jami’an tsaro kan wannan, amma ba sa amsa kiran da muka yi. Watakila hakan ya faru ne saboda ‘yan bindigar na amfani da nagartattun makamai,” inji mazaunin garin.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj