Ibtila’i: Wata Mummunar Gobara Ta Kone Fiye Da Rumfuna 70 A Kasuwar Kingsway Cikin Garin Kano

IMG 115156 12626 1781261533374

Wata mummunar gobara da ta tashi a kasuwar kayayyakin amfanin gida da ofis akan titin Murtala Mohammed a jihar Kano ta ƙone ɗaukacin kasuwar ƙurmus.

Gobarar ta fara ne da misalin ƙarfe 10 na daren jiya Alhamis kamar yanda rahotanni suka bayyana.

Wani mai sana’a a kasuwar ya shaidawa Daily Nigerian mana cewa wutar ta kone kasuwar kurkusa, inda aka yi asarar kaya na miliyoyin Naira.

A cewar sa, har yanzu ba su tantance sanadin faruwar wutar ba, inda ya kara da cewa suna dai tsaye suna jimami, yayin da jami’an hukumar kashe gobara ke kokarin shawo kan lamarin.

Ya kara da cewa wutar ta haura zuwa ginin kamfanin aika sako na DHL da ke makwabtaka da kasuwar inda ta kama rufin Saman ginin shi ma ta kone shi.

Kasuwar, wacce ta ke tsakanin ginin DHL da bankin FCMB a titin Murtala Muhammad, guri ne da ake sayar da kayan amfani da kawata gida da su ka.hada da kujeru, kafet, AC, katifu, firinji, talabijin da kuma kayan kawata ofis.

Kasuwar ta dade a wannan waje sama da shekaru talatin ana gudanar da wannan kasuwancin a wajen.

Allah ya mayar musu da mafificin alherinsa ameen summa ameen

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *